Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Sauya Fasalin Kuɗi: Jam’iyyu 13 Sun Yi Barazanar Ƙaurace Wa Zaɓe 2023

Jam’iyyun siyasa 13 daga cikin 18 a Nijeriya, sun yi barazanar kaurace wa zaɓen shekara ta 2023, matukar Babban Bankin Nijerya ya ƙara wa’adin amfani da tsofaffin kuɗi.

Sun ce ba za su shiga zaɓen ba matuƙar bankin CBN ya sake tsawaita wa’adin amfani da tsofaffin takardun kudin.

Gamayyar ƙungiyar shugabannin jam’iyun sun yaba wa shugaba Muhammadu Buhari a kan sauya fasalin takardun kuɗin, sannan su ka dage a kan cewa dole a tabbatar da tsarin.

Shugaban Jam’iyyar A.A Kenneth Udeze, ya ce akalla jam’iyyu 13 daga cikin 18 ba za su shiga zaɓen da ke tafe ba, matuƙar aka dakatar ko a aka soke ko aka tsawaita wa’adin fara amfani da sabbin takardun naira.

Exit mobile version