Home Labaru Ilimi Sauya Bangaren Ilimi: Gwamnatin Tarayya Ta Sake Barazanar Kama Masu Takardun Digiri...

Sauya Bangaren Ilimi: Gwamnatin Tarayya Ta Sake Barazanar Kama Masu Takardun Digiri Na Bogi

44
0

Gwamnatin tarayya ta ce hukumomin tsaro za su fara farautar mutanen dake rike da takardun kammala karatun digiri na bogi a fadin Najeriya.

Ministan Ilimi Tahir Mamman ne ya bayyana hakan a nan Abuja a ranar Talata yayin karon farko na taron wata uku-uku na ‘yan kasa da masu ruwa da tsaki a bangaren ilmi a Najeriya.

Ministan ya kuma ba ‘yan Najeriya tabbacin gudanar da muhimman sauye-sauye a bangaren ilmin ta hanyar kaddamar da wata taswira mai fannoni 13.

Ya kara da cewar, matukar ana son gudanar da cikakken tsari a fannin ilmi, musamman a matakin firamare da karamar sakandare, ya zama wajibi a samar da sahihan bayanai da za su bunkasa koyon sana’o’in dogaro da kai da za su taimaka wajen rage yawan yaran da basa zuwa makaranta.

Ministan Ilmin ya kara da cewar, gwamnatin tarayya zata dakatar da amincewa da takardun kammala karatun digiri daga karin kasashe irin su, Uganda da Kenya da kuma Jamhuriyar Nijar.

Leave a Reply