Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce ‘yan Nijeriya sun kagara su ga harkar makamashin wutar lantarki ta inganta, ta yadda za a rika gudanar da harkokin kasuwanci da ita.
Buhari ya bayyana haka ne, yayin da ya karbi bakuncin Jakadu daga kasashen Jamus da Ethiopian da su ka hada da Birgitt Ory da kuma Azanaw Tadasse Abreha. Shugaba Buhari, ya bayyana haka ne, jim kadan bayan ya sa hannun a kulla yarjejeniya da kamfanin Siemens domin inganta wutar lantarki a fadin Nijeriya, kamar yadda mai taimaka wa shugaban kasa ta fuskar yada labarai Femi Adesina ya bayyana.
Karanta Wannan: Lantarki: Gwamnati Zata Samar Da Karin Megawati 40 A Wukari