Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Saukaka Sufuri: Shugaba Buhari Ya Bada Umarnin Sakin Manyan Motocin Alfarma

Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bada umarnin sakin sabbin manyan motocin alfarma domin saukaka wa jama’a kalubalen sufuri da rage masu radadin kara farashin man fetur.

Buhari ya mika sakon godiyar sa ga ‘yan Nijeriya, bisa abin da ya kira hakurin da su ka nuna dangane da kalubalen tattalin arziki, sannan ya gode wa ‘yab kungiyar kwadago bisa fahimta da dottako da kuma kishin kasa da su ka nuna.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne, yayin da ya jagoranci wani taro ta yanar gizo daga fadar sa da ke Abuja, ya bukaci ‘yan Nijeriya su rungumi amfani da sinadarin gas a madadin man fetur.

Exit mobile version