Home Labaru Saudiyya Ta Ba ‘Yan Cirani Daman Zama ‘Yan Kasa

Saudiyya Ta Ba ‘Yan Cirani Daman Zama ‘Yan Kasa

158
0

Saudiyya ta ba da izinin zama ɗan ƙasa ga ƴan ƙasar waje da dama da aka bayyana a matsayin mutanen da suka nuna kwazo wajan aikin su.

Ana kallon matakin a matsayin gagarumin sauyi a cikin manufofin masarautar kan ma’aikatan ƙasashen waje.

Saudiyya kamar sauran kasashen yankin Gulf ta shafe fiye da shekaru hamsin tana dogaro da miliyoyin ‘yan kasashen waje a fanin kwadagon ta.

Suna aiki a kowane mataki na tattalin arziki, amma kaɗan ne kawai suka sami wurin zama na dindindin ko ɗan ƙasa.

Yanzu, an ba adadin da ba a fayyace ba damar zaman dan kasa, saboda kwazon su da ƙwarewar su a cewar kamfanin dillancin labarai na ƙasar.

Leave a Reply