Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Saudiyya Ta Ba Wa Najeriya Kyautar Dabino Tan 50 Don Raba Wa ‘Yan Kasa

Kasar Saudiyya ta gabatar da kyautar Ton 50 na dabino mai inganci ga Nijeriya domin karfafa hulda a tsakanin kasashen biyu.

Jakadan kasar Saudiyya a Nijeriya Faisal Alghamdi ya bada kyautar a madadin kasar Saudiyya yayin wani biki da ya gudana a Abuja.

Da ya ke mika kyautar, shugaban tawagar Nezat Talaqi ya ce kyautar daga mai kula da masallatai masu tsarki guda biyu na Sarki Salman Al-Saud ne.

Rahotanni sun ce, taimakon kwanan nan da hukumar ta yi shi ne na ba mutane dubu 48 da 300 Kwando cike da abinci a jihohin Kano da Yobe da kuma Borno, wanda kiyasin say a kai Dala dubu 500.

Da take karban kayan, daraktar yanki a ma’aikatar kasashen waje Janet Olisa, ta gode wa kasar Saudiyya, inda ta ce ‘yan Nijeriya su na godiya matuka da wannan kyauta.

Exit mobile version