Home Labaru Sau 66 Muka Daƙile Kutsen Intanet A Taron Majalisar Zartarwar Najeriya

Sau 66 Muka Daƙile Kutsen Intanet A Taron Majalisar Zartarwar Najeriya

39
0

Ministan harkokin sadarwa da fasahar zamani Isa Ali Pantami, ya ce sau 66 su ke daƙile yunƙurin kutse daga Turai domin ganin yadda majalisar zartarwa ta tarayyar Nijeriya ke tattaunawa ta yanar gizo.

Ya ce duk kutsen da aka yi ƙoƙarin yi, an kai rahotan su ga hukumomin da su ka dace a kan lokaci aka kuma ɗauki matakin da ya dace.

Ministan ya bayyana hakan ne, lokacin gudanar da taron bitar ayyukan gwamnatin Shugaba Buhari daga shekara ta 2015 zuwa 2023 karo na 19.

Ya ce an gabatar da tattaunawar majalisar zartarwar sau 108 tun daga watan Oktoba na shekara ta 2020, domin gudanar da ayyuka da tarurrukan gwamnati ta yanar gizo.