Home Labaru Satar Mutane: Abin Da Ya Sa Muka Zartar Da Hukuncin Kisa A...

Satar Mutane: Abin Da Ya Sa Muka Zartar Da Hukuncin Kisa A Jihar Katsina – Masari

501
0
Aminu Bello Masari, Gwamnan Jihar Katsina
Aminu Bello Masari, Gwamnan Jihar Katsina

Gwamnatin jihar Katsina, ta ce masu garkuwa da mutane da barayin shanu za su fuskanci hukuncin kisa idan aka same su da laifi.

Daukar wannan matakin kuwa, ya biyo bayan gyaran da aka yi wa kundin shari’a na Final-Kod ne a jihar Katsina.

Gyaran dokar, ya kuma hada da daurin rai da rai ga duk wanda aka kama da laifin fyade baya ga biyan diyya.

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya ce matakin da su ka dauka na ma-da satar shanu da garkuwa da mutane a matsayin manyan laifuffuka, ya biyo bayan yadda ta’addanci ke ci-gaba da ta’azzara a fadin jihar.

Jihar Katsina dai ta na daga cikin jihohin arewa maso yammacin Nijeriya da ke fama da rashin tsaro, musamman fashi da makami da kuma garkuwa da mutane.

Leave a Reply