Home Labaru Satar Fasto: ‘Yan Bindiga Sun Bukaci Fansar Naira Miliyan 15 A Jihar...

Satar Fasto: ‘Yan Bindiga Sun Bukaci Fansar Naira Miliyan 15 A Jihar Adamawa

371
0

‘Yan bindigar da su ka yi garkuwa da Fasto Ishaku Ayuba, sun bukaci a biya su Naira miliyan 15 a matsayin kudin fansa kafin su sake shi.

Masu garkuwa da mutanen dai sun yi garkuwa da Ayuba ne a gidan sa da ke Badarissa a karamar hukumar Girie ta jihar Adamawa.

Wani daga cikin ‘yan’uwan Faston da ya bukaci a sakaya sunan sa, ya ce akalla mahara 15 ne su ka kai wa mutumin hari, inda su ka rika harbi ta ko-ina, kuma kafin su tafi da Ayuba sai da su ka ci zarafin iyalin sa.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Adamawa Othman Abubakar ya tabbatar da haka, inda ya ce rundunar ta fara gudanar da bincike domin ceto Fasto Ayuba.

Leave a Reply