Home Labaru Sata A Kasashen Ketare: Gwamnati Ta Bukaci ‘Yan Najeriya Su Yi Taka-Tsan-Tsan A Turai...

Sata A Kasashen Ketare: Gwamnati Ta Bukaci ‘Yan Najeriya Su Yi Taka-Tsan-Tsan A Turai Da Amurka

52
0

Gwamnatin Tarayya ta shawarci ’yan Najeriya masu shirin zuwa Amurka da Ingila da sauran kasashen Turai su yi hankali da barayin da za su iya yi musu sata a can.


Gwamnatin ta shawarci ’yan kasar nan su yi takatsantsan da mutanen da za su iya sace musu fasfo da kudi da sauran muhimman abubuwansu a kasashen.


Minista Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayar da shawarar ranar Litinin, a lokacin da yake jawabi kan nasarorin Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari , karo na
biyar aAbuja.


A cewarsa, a dan tsakanin nan, ana samun karuwar rahotannin yawan sace wa ’yan Najeriya kayayyakinsu, ciki har da fasfo dinsu.


Shawarar na zuwa ne wata daya bayan kasashen Amurka da Birtaniya sun gargadi ’yan kasarsu cewa za a iya kai hari a Abuja.