Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar da cewa a yanzu haka an kusa kammala aikin katafaren Kamfanin sarrafa karafa na Ajaokuta dake jihar Kogi da zai samar wa ‘yan Nijeriya dubu 500 guraben aikin yi.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, wanda ya wakilci shugaban kasan, ya bayyana haka a wajen kaddamar da yakin neman zaben gwamna na jam’iyyar APC a Lokoja, babban birnin jihar Kogi.
Ya ce shugaba Tinubu ya kuma yi alkawarin mayar da hankali wajen ganin an kammala aikin Kamfanin domin zai bunkasa tattalin arzikin Najeriya ta hanyar janyo masu zuba jari kai tsaye FDI da kuma samar da hanyar ingantaccen yanayin kasuwanci da ake bukata domin kowane fanni ya samu ci gaba.
Da yake jawabi ga dimbin jama’a a Lokoja, Kashim Shettima, a wata sanarwa da mai magana da yawun sa, Stanley Nkwocha, ya fitar, ya kuma bayyana cewa, Tinubu ya jajirce wajen ganin an kammala aikin kogin Neja da kuma aikin hanyar Kabba zuwa Lokoja da Abuja zuwa Lokoja.
You must log in to post a comment.