Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Sarkin Kano Ya Bukaci Tinubu Ya Kafa Ma’Aikatar Harkokin Addinai

Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya
bukaci zababben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kafa
ma’aikatar harkokin addini domin inganta tattaunawa tsakanin
mabiya addinai da zaman lafiya a Nijeriya.

Basraken ya yi kiran ne, a wajen bikin kaddamar da Jagororin addini da kungiyar agaji ta Action Aid ta shirya a Kano.

Sarkin, wanda ya samu wakilcin Hakimin Nasarawa Babba Dan-Agundi, ya ce za a dora wa ma’aikatar ayyukan da su ka shafi inganta fahimtar addini da fahimtar juna a tsakanin ‘yan Nijeriya, ya na mai bayyana Kano a matsayin tushen zaman lafiya, inda mabiya addinai daban-daban ke zaune lafiya da juna.

Sarkin ya bayyana tattaunawar tsakanin mabiya addinan a matsayin wadda ta dace domin samar da zaman lafiya, ya na mai cewa Kano ta dade ta na rike da matsayi mai girma wajen karbar mabiya addinai daban-daban.

Exit mobile version