Home Home Sarki Charles Ya Kaddamar Da Shirin Samar Da Aikin Yi A Nijeriya

Sarki Charles Ya Kaddamar Da Shirin Samar Da Aikin Yi A Nijeriya

105
0

Mai Martaba Sarkin Ingila Charles na Uku, ya kaddamar da shirin magance rashin aikin yi tare da samar da ayyukan yi ga matasan Nijeriya.

Bayanin hakan ya fito ne, yayin bikin baje kolin daukar ma’aikata na Prince’s Trust International a Legas.

An dai gudanar da bikin baje kolin ne tare da hadin gwiwar kungiyar tuntubar ma’aikata ta Nijeriya da kuma da cibiyar bunkasa kwarewa da sana’o’in hannu ta FSD.

Babban jami’in gudanarwa na bikin baje kolin daukar ma’aikata Mista Will Straw, ya ce karancin ayyukan yi kalubale ne a duniya ba ma ga Nijeriya kadai ba.

Mista Straw ya yi nuni da cewa, matasan Nijeriya su na fuskantar matsalolin kwarewa da ayyukan yi, kuma sama da yara miliyan 10 ba su zuwa makaranta.

Ya ce burin su a Nijeriya shi ne, samar da damarmakin da za su canza rayuwar matasa da nufin tallafa wa dubban matasa kai-tsaye a shekaru masu zuwa.

Leave a Reply