Home Labaru Sarautar Kano: Sarkin Bichi Ya Bukaci Kanawa Su Rungumi Abinda Allah Ya...

Sarautar Kano: Sarkin Bichi Ya Bukaci Kanawa Su Rungumi Abinda Allah Ya Kawo

1985
0
Alhaji Aminu Ado Bayero, Sabon Sarkin Bichi Mai Martaba

Sabon sarkin Bichi mai martaba alhaji Aminu Ado Bayero ,ya ce ya kwana da sanin cewa masarautar Kano na taimakawa wajen hada kan al’umma, domin haka ba shi da wani buri na ganin an rarraba masarautar mai tsohon tarihi.

Sarkin ya bayyana hakan ne ga kafar yada labarai ta BBC jim kadan bayan kammala taron godiya da gwamnatin jihar ta shirya inda ya kara da a rayuwarsa ba ya da wani buri na ganin an rarraba masarautar Kano, domin sun san ta na kawo hadin kai na al’umma baki daya.

Sarki Aminu Ado na daya daga cikin sabbin sarakuna guda hudu da gwamnatin ta nada bayan ta kirkiri karin masarautu domin rage matsalolin ci gaba da  suka yi nauyi a hannun masarautar Kano, kamar yadda gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar  Ganduje ya bayyana.

Sarkin Bichi ya ce duk da ba shi da burin raba masarautar, amma wasu dalilai da gwamnati ta hanga har kuma a kawo wannan sauyi, babu wani abu da al’umma za su yi, sai dai su karbi wannan yanayi da Allah ya kawo. Kafin nadinsa a matsayin sabon sarki, Aminu Ado Bayero na rike da sarautar Wamban Kano ne a masarautar Sarki Sanusi na II.

Leave a Reply