A mako mai zuwa ne ake sa ran majalisar dokoki ta jihar Kano za ta dauki matsaya a kan bukatar da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar na yin gyara ga dokar Masarautun Kano ta shekarar 2019.
Gwamna Ganduje dai ya gabatar wa Majalisar Dokokin ta jihar Kano bukatar yi wa dokar Masarautun jihar ta shekarar 2019 kwaskwarima, domin ganin an kara Sarkin Dawaki Babba a cikin masu zaben Sarkin Kano.
Matakin dai ya na zuwa ne, yayin da Masarautar Kano ke jiran amsar gwamnati a hukumance a kan bukatar nada Aminu Babba Dan-Agundi a matsayin Sarkin Dawaki Babba, da kuma Alhaji Sanusi Ado Bayero a matsayin Wamban Kano.
Marigayi Sarkin Kano Ado Bayero ne ya sauke Aminu Babba daga sarauta, yayin da tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya sauke Lamido Ado Bayero.