Home Labaru Sarakunan Jihar Ekiti Sun Maka Gwamna Fayemi Kotu

Sarakunan Jihar Ekiti Sun Maka Gwamna Fayemi Kotu

522
0
Kayode Fayemi, Gwamna Jihar Ekiti
Kayode Fayemi, Gwamna Jihar Ekiti

Manyan sarakuna 16 da ke Sarakunan jihar Ekiti sun kai karar gwamna Kayode Fayemi a gaban kotu, biyo bayan nadin da ya yi na shugaban majalisar Sarakuna ta jihar.

Sarakunan dai sun nuna rashin jin dadin su, game da yadda gwamnan ya zakulo mutumin da ba ya cikin su a matsayin shugaban majalisar Sarakuna.

A cewar Sarakunan, gwamnatin jihar ta saba wa dokar sarauta wajen nada Sarki Adebanji Alabi a kan kujerar shugaban majalisar Sarakunan Ekiti.

Daga cikin wadanda Sarakunan su ka hada a karar da su ka shigar kotu, akwai Kwamsihinan shari’a kuma babban Lauyan gwamnatin jihar Ekiti Wale Fapohunda da kuma Sarkin Oye.

Sarakunan sun bayyana wa kotun cewa, su kadai ne asalin sarakunan-yanka a jihar Ekiti, don haka su ka ce nada Adebanji Alabi a matsayin shugaban su ya saba wa doka tare da wulakanta gadon sarauta, don haka ba za su halarci bikin rantsar da shi ba.

Leave a Reply