Home Labaru Sanyin Gwiwa: Sojojin Nijeriya Kaɗai Ba Za Su Iya Maganin Boko Haram...

Sanyin Gwiwa: Sojojin Nijeriya Kaɗai Ba Za Su Iya Maganin Boko Haram Ba — Gwamnoni

234
0

Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya kuma Gwamnan jihar
Ekiti Kayode Fayemi, ya ce harkar tsaro ta fi ƙarfin sojojin
Nijeriya su kaɗai.

Kayode Fayemi, ya ce guwawun gwamnoni a sanyaye su ke a
jihohin su, sannan kuma sojoji kaɗai ba za su iya cin nasara a
yaƙi da Boko Haram ba.

Gwamnan ya bayyana haka ne, yayin da tawagar su ta je
ta’aziyya ga Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno, bayan
Boko Haram ta yi wa akalla manoma 100 yankan rago.

Ya ce gwamnoni ba za su iya yin maganin matsalar tsaro da ke
addabar wasu yankunan jihohin su ba.

Kayode Fayemi, ya ce abin da ya bayyana ƙarara shi ne sojoji ba
za su iya magance wannan matsalar su kaɗai ba, shawara kawai
ita ce, ya kamata a gayyato maƙwaftan ƙasashe waɗanda babu
mamaki sun fi mu sanin yadda ake yaƙin daidaita ƙasa.