Home Labaru Sanatan Borno Ya Ja-Kunnen Sojoji A Kan Maida Tsofaffin ‘Yan Ta’addan Boko...

Sanatan Borno Ya Ja-Kunnen Sojoji A Kan Maida Tsofaffin ‘Yan Ta’addan Boko Haram ‘Yan Lele

151
0
Sanata Ali Muhammad Ndume

Dan majalisar dattawa mai wakiltar Borno ta kudu Sanata Ali Muhammad Ndume, ya shawaci sojoji su rika taka-tsantsan da ‘yan ta’addan da ke mika kansu, saboda a cewarsa ya kamata ne a rika binciken tsofaffin mayakan a tsanake.

Ndume, ya bada shawarar ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels, inda ya yabi sojojin Nijeriya, ya kuma nemi a hanzarta yin maganin masu tada kafar baya a yankin Arewa maso gabas.

Sanatan ya kuma yi nuni da cewa, nasarorin da sojojin Nijeriya ke samu a ‘yan kwanakin nan ya tabbatar da cewa, matukar aka samu wadatattun kayan yaki za a yi galaba kan ‘yan ta’addan.

Sanata Ndume ya kuma gargadi jami’an tsaron kada su yi wasa da tubabbun ‘yan ta’addan, yana mai cewa su fara maida hankali a kan al’ummar yankin.

Leave a Reply