Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Samun Rauni: Rodri Na Man City Zai Yi Jinya Zuwa Ƙarshen Kakar Bana

1cec4720 7ce0 11ef bf4b ef19cfbf3842.jpg

1cec4720 7ce0 11ef bf4b ef19cfbf3842.jpg

Dan wasan tsakiya na Manchester City, Rodri ba zai sake buga wasa a kakar wasanni ta bana ba.

Rodri mai shekara 28 ya ji rauni ne bayan karon da ya yi da Thomas Partey, a wasan da ƙungiyar sa ta tashi 2-2 da Arsenal a ƙarshen mako.

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce yanzu haka an yi wa ɗan wasan tiyata a gwiwar sa kuma ba zai sake buga wasa a wannan kaka ba.

Exit mobile version