Dan wasan tsakiya na Manchester City, Rodri ba zai sake buga wasa a kakar wasanni ta bana ba.
Rodri mai shekara 28 ya ji rauni ne bayan karon da ya yi da Thomas Partey, a wasan da ƙungiyar sa ta tashi 2-2 da Arsenal a ƙarshen mako.
Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce yanzu haka an yi wa ɗan wasan tiyata a gwiwar sa kuma ba zai sake buga wasa a wannan kaka ba.