Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Samfuri Ne Kawai Muka Nuna Ba Mun Kaddamar Da Yadda Jirgin Zai Kasance Ba Ne – Hadi Sirika

Tsohon ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika, ya ce salon
talla ne daga masu hannun jarin kamfanin ya sa a ka kawo
jirgin da ya sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke
Abuja kuma hakan ba sabon abu ba ne.

Hadi Sirika, ya ce gwamnatin Nijeriya ta na da hannun jari kashi 5 cikin 100 kacal a kamfanin, sauran kasha 95 na ‘yan kasuwa ne da mafi tsoka na Ethiopia ne.

A zaman karshe da kwamitin kula da sufurin jiragen sama na majalisar dattawa ta yi a kan kamfanin jirgin na Nijeriya, ya nuna cewa ba a gayyace su kaddamarwar ba ko ba a sanya su a tsarin ba gaba daya.

Shugabar kwamitin Biodum Olujimi, ta ce gaba daya an gudanar da tsarin Nijeriya a boye, inda aka gabatar da shi cikin kumbiya-kumbiya a matsayin jirgin sama na kasa, lamarin da ya yi hannun riga da ka’idojin aikin jirgi da dokokin kasa da kasa da ke jagorantar harkar jiragen sama.

Exit mobile version