Amurka ta sake hawa kujerar naƙi game da buƙatar ba yankin Falasɗinu damar zama kasa mai cikakken ƴanci da kuma kujerar dindindin a zauren Majalisar.
Yayin zaman kaɗa ƙuri’ar da ya gudana a jiya Alhamis a birnin New York wanda kasashen Birtaniya da Switzerland suka kauracewa, kasashe 12 ne suka goyi bayan ƙudirin yayinda Amurkan ta sake jan tunga game da batun.
Bayan da ta yi watsi da ƙuri’un da takwarorin ta suka kaɗa, Amurkan ta bakin mataimakin jakadan ta a zauren Robert Wood ya ce yankin na Falasɗinu ba shi da zaɓin da wuce sulhuntawa da Isra’ila game da bukatar samun ƴanci ko kuma zama ƙasa mai cin gashin kan ta.
A cewar Wood dukkanin yunƙurin da kasashe ke fafutukar yi ba zai haifarwa Falasɗinu ɗa mai ido ba, domin kuwa wannan yunƙuri ba shi ne zai kai yankin ga zamowa ƙasa mai cikakken iko ba.
Zaman kaɗa ƙuri’ar na zuwa ne bayan Isra’ila ta shafe fiye da watanni 6 ta na luguden wuta a zirin Gaza wanda ya kashe Falasɗinawa fiye da dubu 33 tare da tagayyara al’ummar yankin baya ge jefa su a matsanancin halin bukatar agaji.
Akalla kashi 2 bisa 3 na ‘yan kwamitin tsaro na Majalisar ko kuma kasashe 9 cikin 15 na zauren ake bukata su kada ƙuri’ar amincewa ƙudiri gabanin kasancewar sa doka, sai dai a wannan karon lamarin ya sha bamban.