Home Labaru Samar Da Tsaro: ‘Yan Sanda Sun Kama Yan Ta’adda 71 A Jihar...

Samar Da Tsaro: ‘Yan Sanda Sun Kama Yan Ta’adda 71 A Jihar Kaduna

353
0

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta cewa ta samu nasarar kama wasu mutane 71 a cikin makonni uku da suka gabata wadanda ake zargi da aikata miyagun laifuka daban daban.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ali Janga ya bayyana haka ga manema labarai, inda ya kara da cewa wajibi ya sanar da ‘yan jarida irin ayyukan da rundunar sa ta ke yi, da kuma irin cigaba da su ke samu a yaki da su ke yi  da ayyukan ta’addanci a jihar.

Kamfanin dillancin labaran Nijeriya NAN ya ruwaito cewa, mutanen 71 da aka kama an same su da a kan laifuka daban daban, wadanda suka hada da fashi da makami da garkuwa da mutane da kuma laifin kisan kai.

Bugu da kari, daga cikin su akwai wadanda aka kama da laifin mallakar muggan makamai ba bisa ka’ida ba da tu’ammuli damiyagun kwayoyi da sauran ababen da aka haramtawa mutane amfani da su.

Leave a Reply