Home Labaru Samar Da Tsaro: Sojoji Sun Yi Wa ‘Yan Bindiga Ruwan Wuta A...

Samar Da Tsaro: Sojoji Sun Yi Wa ‘Yan Bindiga Ruwan Wuta A Borno Da Zamfara

55
0

Rundunar sojin saman Najeriya ta ce ta kashe ‘yan bindiga masu yawa a yayin wasu hare-hare ta sama da ta ƙaddamar kan maɓoyar ‘yan ta’adda a wasu sassan ƙasa.

Cikin wata sanarwar da rundunar ta fitar a  Lahadin nan, mai ɗauke da sa hannun daraktan hulɗa da jama’a na rundunar, Air Commodore Edward Gabkwet, ta ce dakarun sojin ƙarƙashin haɗin gwiwar rundunonin Hadin Kai da ta Hadarin Daji sun kai hare-hare kan ‘yan ta’adda a Bukar Meram, kusa da Tafkin Chadi a jihar Borno da kuma yankin Sangeko a jihar Zamfara.

Air Commodore Edward Gabkwet, ya ce rundunar ta ƙaddamar da hare-haren ne bayan da ta samu bayanai game da sauya matsuguni da ‘yan bindigar ke yi.

Ya ce harin farko an kai shi a lokacin da ‘yan bindigar ke ƙaura daga Suwa zuwa yankin Bukar Meram, domin shirya kai hare-hare kan fararen hula da sojoji.

Sanarwar ta ƙara da cewa harin ya samu nasarar halaka ‘yan ta’addan masu yawan gaske tare da lalata babura fiye da 40 da motocin da ke dakon makamai ga ‘yan bindigar.