Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Samar Da Rugage: Kwasari Ya Bukaci A Yi Watsi Da Barazanar Kungiyoyin Arewa

Fadar shugaban kasa ta ce ba a dakatar da shirin inganta al’amarran kiwo da Gwamnatin Tarayya ke son aiwatarwa ba.

Yayin da ta ke shawartar ‘yan Nijeriya cewa kada su damu da wa’adin kwanaki 30 da gamayyar kungiyoyin arewa ta bada a kan shirin Rugage, fadar shugaban kasa ta shawarci kungiyar ta mutunta ofishin shugaban kasa saboda ya yanke hukunci ne domin ci-gaban kasa.

Babban mai bada shawara a kan harkokin gona a ofishin mataimakin shugaban kasa Dakta Andrew Kwasari ya bayyana wa manema labarai haka a Abuja, yayin wani taro da aka shirya wa shugabannin kungiyar Miyyetti Allah da jami’an ta a jihohi takwas a matsayin shirin wayar da kai.

Babban mai bada shawara a kan harkokin gona , ofishin mataimakin shugaban kasa Dakta Andrew Kwasari

Kakakin kungiyar arewa Abdul-Azeez Suleiman, ya ce da wasu shugabannin yankin arewa ake hada baki domin a nakasa yankin, sai dai Kwasari ya yi watsi da wannan barazana, inda ya ce mafi rinjayen ‘yan Nijeriya sun goyi bayan shugaba Buhari a kan dakatar da shirin gina Rugagen.

Exit mobile version