Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya bukaci kotun sauraren ƙararrakin zaɓe ta tsige shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu daga kujerar sa.
A cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, Atiku ya shaida wa shugaba Tinubu da jam’iyyar APC cewa sama ba za ta faɗo ba idan kotu ta tsige Bola Tinubu daga kujerar sa.
Atiku Abubakar, ya roƙi kotun ta yi ta hanzarta wajen cika roƙon da ya yi na neman a soke nasarar da Tinubu ya yi a zaɓen da ya gabata, ya na mai cewa, ba hujja ba ce kotun ta ƙi soke nasarar Tinubu don kawai ba a taɓa yin irin haka a baya ba.
Haka kuma, Atiku ya yi kira ga kotun cewa kada barazana ko wani zare idanu su hana ta yanke hukunci bisa adalci, kawai ta yanke hukunci yadda ya ke duk abin da zai faru ma ya faru.
A karshe ya zargi hukumar zaɓe a kan gaza bada sahihin sakamakon zaɓe, ya na mai cewa shaidar da ta gabatar a gaban kotu ya tabbatar da cewa ba ta tafiyar da zaɓen yadda ya kamata ba.