Al’ummar Musulmi na kasar Mali, sun yi bikin karamar salla, bayan sun samu tabbacin ganin jaririn watan Shawwal a yammacin ranar Lahadin da ta gabata.
A cikin wata sanarwa da ministan harkokin addini na kasar ya raba wa manema labarai, gwamnati ta tsaida ranar Litinin 3 ga watan Yuni a matsayin ranar karamar Sallah a fadin kasar Mali.
Sanarwar ta Ambato ministan ya na cewa, an ga watan a wasu wurare na wasu yankunan kasar da su ka hada da Kati da kuma Bamako fadar gwamnatin kasar, don haka sanarwar ta ce ya zama wajibi a yi sallah ranar ta Litanin a fadin kasar baki daya.
Al’ummar kasar Mali dai sun dauki azumin Ramadan ne a ranar Lahadi, 4 ga watan Mayu, sabanin yadda akasarin kasashen musulmi a fadin duniya su ka tashi da azumi a ranar Litanin.