Home Labaru Sakamakon Zabe: Abba Kabir Yusuf Ya Maka Ganduje Kotun Kararrakin Zabe

Sakamakon Zabe: Abba Kabir Yusuf Ya Maka Ganduje Kotun Kararrakin Zabe

265
0

Dan takarar kujerar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar PDP Abba Kabir Yusuf, ya shigar da kara a gaban kotun kararrakin zabe da ke zama a cikin birnin Kano.

Abba Kabir Yusuf ya shaida wa manema labarai cewa, sun je kotu ne domin gabatar da duk takardun su na korafe-korafe da lauyoyin su su ka tsara a kan zabubbukan da su ka gudana.

Ya ce a zaben da aka yi ranar 9 ga watan Maris, hukumar zabe ta kasa ta sanar da sakamakon, inda ta ce jam’iyyar PDP ke kan gaba, amma daga bisani ta ce zaben bai kammala ba, inda aka sake yin wani a ranar 23 ga watan na Maris aka kuma bayyana Ganduje a matsayin wanda ya samu nasara.

Abba Kabir ya kara da cewa, sun dauki matakin kin amincewa da sakamakon zaben ne, saboda zabe ne da kowa a Nijeriya da ma wasu kasashen duniya su ka yi Allah-Wadai da shi.

Leave a Reply