Home Labaru Kiwon Lafiya Safarar Kwayoyi: Hukumar NDLEA Ta Gargadi Muhammad Wakili

Safarar Kwayoyi: Hukumar NDLEA Ta Gargadi Muhammad Wakili

689
0

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA, ta gargadi kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano Muhammadu Wakili ya zare hannun shi daga sha’anin yaki da fataucin miyagun kwayoyi ko ya fuskanci hukuncin shari’a.

Kwamandan hukumar na jihar Kano Ibrahim Abdul, ya ce sashe na 3 da 1  cikin baka na kundin dokokin hukumar NDLEA, ya ba su damar jagorancin duk al’amuran da su ka shafi tu’ammali da miyagun kwayoyi a Nijeriya.

Wannan rashin jituwa dai ta zo ne, sakamakon furucin da Wakili ya yi cewa jami’an ‘yan sanda sun yi nasarar kama kwalayen Tramadol 303 a makon da ya gabata.

Sai dai Ibrahim Abdul ya bayyana wa manema labarai cewa, ‘yan sanda sun karbe wani magani mai suna ‘Diclofenac’, wanda ke maganin ciwo jiki amma ba Tramadol ba.

Ya hakan ya taba faruwa a watan Fabrairu, inda hukumar ‘yan sanda ta ce ta karbe kwayar Tramadol, amma da su ka bincika sai su ka samu maganin zazzabin cizon sauro ne da wani makamancin sa.

Leave a Reply