Gwamnatin Najeriya ta ce yanzu haka ‘yan Najeriay 446 ne ke tsare a gidajen yarin kasar Hadaddiyar Daular Larabwa saboda aikata laifuffukan da ke da nasaba da safarar miyagun kwayoyi da kuma wasu laifuffuka.
A jawaban da ya gabatar gaban taron ‘yan Najeriya mazauna kasar ta Hadaddiyar Daular Larabawa, yayin wata ganawar su da Shugaba Muhammadu Buhari a ziyarar da yanzu haka ya ke ci gaba da yi a kasar, Jakadan Najeriyar a birnin Dubai, Ambasada Mohammed Dansanta Rimi, yace akwai tarin ‘yan Najeriya da ke aikata ayyukan assha a kasar.
Kalaman na Ambasada Mohammed Dansamta Rimi, na zuwa ne makwanni kalilan bayan kame wasu ‘yan Najeriyar guda 5 da ake zargi da laifin fashi da makami a Kasar.
Ka zalika ko cikin watan jiya an yankewa wasu tarin ‘yan Najeriya hukuncin kisa wasu kuma na daure su a gidajen yarin Saudiya bayan samun su da aikata ba dai dai ba.