Gwamna jihar kano Abdullahi Ganduje ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada nagartattun mutane sabuwar majalisar sa da sai kafa nan bada dadewa ba.
Ganduje ya bada wannan shawara ce a lokacin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai jim kadan bayan sun yi wata ganawar da mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo a Abuja.
Gwamna Ganduje ya ce ya je fadar Shugaban kasa ne domin sanar da mataimakin shugaban kasa cewa, an kamala komai domin ziyarar da zai kai jihar Kano a ranar Asabar, 13 ga watan Afrilu. Ganduje ya ce ya kuma sanar da Osinbajo cewa, al’ummar jihar Kano sun shirya domin tarbar sa sakamakon yadda su ke farin cikin cewa, jam’iyyar APC ce ta lashe zaben jihar, kuma baya dar-dar da shigar da kara da jam’iyyar PDP ta yi na kalubalantar sakamakon zaben gwamnan jihar
You must log in to post a comment.