Home Home Sabuwar Hukumar Hana Yaduwar Makamai Za Ta Dauki Mutum 300,000 Aiki

Sabuwar Hukumar Hana Yaduwar Makamai Za Ta Dauki Mutum 300,000 Aiki

1
0

Sabuwar hukumar yaki da yaduwar manya da kananan makamai ta kasa NATCOM, ta ce ta kammala shirin daukar mutane dubu 300 aiki a fadin Nijeriya.

Hukumar ta ce, za ta dauki mutanen ne sannan ta horar da su domin dakile yaduwar makamai a daidai lokacin da ake fama da kalubalen tsaro.

Mai rikon mukamin shugaban hukumar Otunba Adejare Rewane ya sanar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce hukumar za ta dauki mutane dubu 7 aiki a kowace Jiha da kuma Birnin Tarayya Abuja.

Ya ce daukar aikin zai taimaka wajen rage matsalar rashin aikin yi, kuma za su hada kai da sauran jami’an tsaro domin ganin an sami nasara.

Otunba Adejare, ya ce masu son a dauke su aikin su rika duba jaridu domin ganin bayanai da ka’idoji, amma za su fi ba matasa masu jini a jika fifiko wajen daukar aikin.