Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin ta zartas da wata doka da za ta kyautata tsarin kariya na kasashen waje a kasar Sin, inda ta tanadi dokokin da kotunan kasar Sin za ta bi wajen gudanar da shari’ar farar hula da suka shafi wata kasa da kadarorinta.
Kakakin ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambaya game da dokar kare hakkin kasashen waje na kasar Sin, wadda zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ya yi nazari a kai tare da zartar da shi a wani zama na baya-bayan nan.
Dokar ta daidaita matsayin kasar Sin na baya-bayan nan na tabbatar da cikakkiyar kariya ga kasashen waje, ta kuma ba da izinin ga kotuna a kasar Sin su saurari kararrakin da suka shafi kasashen waje.
You must log in to post a comment.