Home Labaru Sabon Zubi: Ganduje Ya Sallami Duk Manyan Sakatarorin Ma’aikatun Jihar Kano

Sabon Zubi: Ganduje Ya Sallami Duk Manyan Sakatarorin Ma’aikatun Jihar Kano

386
0
Abdullahi Ganduje, Gwamna jihar Kano
Abdullahi Ganduje, Gwamna jihar Kano

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano, ya sallami duk manyan sakatarorin ma’aikatun gwamnatin jihar daga aikin su zuwa ranar Laraba 8 ga watan Mayun 2019.

A cikin wasikar da aka aike mai dauke da sa hannun shugaban ma’aikata na jihar Mohammed Awwal-Na’iya, Ganduje ya bukaci su mika aiki ga manyan direktocin ma’aikatunsu ko hukumomin su.

Gwamnan, ya shawarci duk manyan sakatarorin da aka sallama da sauran daraktoci da ke mataki na 16 ko 17 masu sha’awar kujerar su mika takardun neman aiki ga ofishin shugaban ma’aikata na jihar kafin karfe hudu na yammacin ranar 9 ga watan Mayu. Wasikar ta ce, kamar yadda ya ke a tsarin gwamnati mai ci na kawo sabbin tsare-tsaren inganta aiki da kawo sabbin jini a manyan mukamman gwamnatin jihar, gwamnati ta bada umurnin sallamar duk manyan sakatarorin ta ba tare da bata lokaci ba.

Leave a Reply