Kungiyoyin kwadago ta NLC da TUC sun bukaci hukumomi da cibiyoyi daga matakin tarayya da jihohi su gaggauta kaddamar da sabon tsarin mafi karancin albashin ma’aikata na naira dubu 30 da shugaban kasa Muhammadu Buhari yua sanyawa hannu.
A cikin wasu sanarwa daban-daban kungiyoyin sun yabawa shugaban kasa kan matakin da ya dauka na sanya hannu a dokar, da aka dade ana jira.
Kungiyar ta ce sanya hannu kan sabon tsarin albashin shine kashin farko, abin da ya rage shine kiraye-kiraye domin ganin an kaddamar da shi yadda ya kamata.
Sannan ta bukaci hukumomi da cibiyoyin gwamnatin tarayya da na jihohi da su fara tattaunawa da kungiyoyin da abin ya shafa domin tabbatar da ana yin abin da ya kamata.
A nata bangaren kungiyar TUC ta ce sabon tsarin mafi karancin albashin ma’aikatan zai taimaka wajen karawa ma’aikata kwarin gwiwar gudanar da ayyukansu.
You must log in to post a comment.