Home Labaru Sabon Sarkin Gaya: Gwamnatin Jihar Kano Ta Nada Aliyu Ibrahim Abdulkadir

Sabon Sarkin Gaya: Gwamnatin Jihar Kano Ta Nada Aliyu Ibrahim Abdulkadir

69
0

Gwamnatin jihar Kano ta nada Aliyu Ibrahim Abdulkadir a matsayin sabon sarkin Gaya.

Sakataren gwamnatin jihar Alhaji Usman Alhaji kuma wazirin Gaya sannan shugaban masu zaben sarkin ne ya sanar da nadin sabon sarkin a ranar Lahadi.

Yace dokar masarautar Kano ta 2020 da aka yi wa kwaskwarima ta amince da nadin Aliyu Ibrahim Abdulkadir Gaya a matsayin sabon sarkin Gaya.

An nada sabon sarkin ne bayan rasuwar Sarkin Gaya Alhaji Ibrahim Abdulkadir a makon da ya gabata.

Sabon Sarkin Gaya Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir dan Marigayi Sarkin Gaya ne Alhaji Ibrahim Abdulƙadir, Kuma shi ne dansa na biyu, Kafin Naɗin sa dai shi ne Ciroman Gaya.