Home Labaru Sabon Rikici Ya Kunno Kai A Jam’iyyar APC

Sabon Rikici Ya Kunno Kai A Jam’iyyar APC

466
0
APC

Wutar rikici na ruruwa a jam’iyyar APC, yayin da shugabannin jam’iyyyar na jihohi 36 da birnin tarayya su ka yi Allah-Wadai da abin da su ka bayyana a matsayin rashin karramawar da ta dace a jam’iyyar.

Shugabannin dai sun yi korafin cewa, hatta wadanda suka kafa jam’iyyar da wadanda su ka sha wahala wajen ganin nasarar ta a matakai daban-daban duk an yi watsi da su, yayinda wasu da su ka zo daga sama ke cin moriyar abin da ba su shuka ba.

A cikin wani jawabin bayan taro da aka fitar a Abuja, shugabannin sun ce an doshi magoya bayan jam’iyyar APC a fadin Nijeriya da abin kunya da tozarci a matakai daban-daban, inda su ka ce an yi watsi da tsarin jam’iyyar baki daya.

Jawabin dai, ya na dauke da sa hannun shugaba da sakataren kungiyar Ali Bukar Bolari da Ben Nwoye., wadanda dukkan su shugabann jam’iyyar ne a jihohin Borno da Enugu. A cikin jawabin, sun ce anyi watsi da shugabannin da ke jan ragamar jam’yyar a jihohin su kwata-kwata, musamman ta bangaren nade-naden mukaman tarayya.