Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Sabon Kamfanin NNPC: Shugaba Buhari Ya Nada Hukumar Gudanarwa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a matsayinsa na Ministan harkokin man fetur ya bayar da umarnin mayar da kamfanin mai na NNPC a matsayin wanda zai iya ba da dama a zuba hannun jari, wato Nigerian National Petroleum Company Limited a turance.

Wannan ya yi dai-dai da bangare na 53 (1) na Dokar Man Fetur ta 2021, wadda ta bukaci Ministan Man Fetur ya mayar da kamfanin wanda za a iya zuba jari cikin wata shidda bayan sa hannu kan dokar.

Haka kuma, Shugaba Buhari ya nada darektocin hukumar gudanarwar kamfanin da suka hada da sanata Ifeanyi Ararume a matsayin shugaba yayin da Mele Kolo Kyari ne shugaban kamfanin sannan Umar Ajiya ne babban darektan da ke kula da harkokin kudi.

Sauran mabobin hukumar sun hada da Dokta Tajudeen Umar, da Misis Lami Ahmed, da Mallam Mohammed Lawal, da Sanata Margaret Chuba Okadigbo, da Barrister Constance Harry Marshal da kuma Cif Pius Akinyelure.

Shugaba Buhari ya bukaci shugaban kamfanin man na Najeriya NNPC, Malam Mele Kolo Kyari, ya dauki matakan da suka dace don tabbatar da sauya kamfanin.

Exit mobile version