Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike, ya musanta rahotannin da ke cewa gwamnatin sa ta rushe wani masallaci a jihar.
Nyeson Wike ya shaida wa manema labarai cewa, gwamnatin jihar ta hana masu son gina masallacin yin gini, inda mutanen su ka garzaya kotu, amma gwamnati ta samu nasara a kan su.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne, wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta na zamani, ya nuna taron masallata su na sallar Juma’a a wani wuri da aka ce masallaci ne da gwamnatin jihar Rivers ta rushe a yankin Trans Amadi na birnin Fatakwal.
Lamarin dai ya janyo cece-ku-ce, tare da ta da jijiyoyin wuya a kafafen sada zumunta, musamman tsakanin al’ummar kudu da arewacin Nijeriya ko kuma tsakanin musulmi da kiristoci.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/libertytvnews
Twitter: https://twitter.com/libertytvnews
Instagram: https://instagram.com/libertytvng
Liberty Radio 103.3 FM Abuja Kai Tsaye A Yanar Gizo ??
zeno.fm/libertyradioabuja
Tashar Ƴanci 103.1 FM Kaduna Kai Tsaye A Yanar Gizo ??
zeno.fm/tasharyancikaduna ?
Kira ??? +1-701-719-6971 don suraren (Tashar Ƴanci 103.1 FM Kaduna) kai tsaye ta wayar hannu. Musamman Ga Waɗanda Suke Ƙasar Amurka.
Kuna iya turo mana labari ko shawara a: info@libertytvradio.com
You must log in to post a comment.