Kwamitin yaƙin Neman Zaɓen Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, ya yi kira ga Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya NDLEA, ta gaggauta binciken Bola Tinubu dangane da zargin harƙallar miyagun ƙwayoyin da aka yi masa tun tuni.
Wata Sanarwa da kwamitin ya fitar, ta ce ganganci ne kuma mummunan kuskure idan aka zaɓi wanda aka zarge shi da tu’ammali da miyagun ƙwayoyi ƙiri-ƙiri a a matsayin shugaban Nijeriya.
Ta ce idan aka bari Tinubu ya zama shugaban ƙasa, to Najeriya za ta afka cikin muggan laifuffukan da manyan ‘yan ƙwaya ke haddasawa.
Sanarwar ta cigaba da cewa, Nijeriya za ta yi kuskure idan aka zaɓi mutumin da ake zargi da harƙallar miyagun ƙwayoyi, domin Najeriya za ta iya komawa a hannun ‘yan ƙwaya, wadanda za su riƙa tafka muggan laifuffukan da za su lalata ta fiye da yadda aka yi wa Colombiya.