Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Rundunar Sojin Nijeriya Ta Kafa Kotun Hukunta Sojoji

Kwamandan rundunar sojin da ke fafatawa da mayakan kungiyar Boko Haram Benson Akinroluyo ya bude kotun hukunta sojojin da su ka aikata laifuffuka.

Nigerian-Army-Court

Benson ya bude kotun ne, ganin cewa akwai sojojin da su ka aikata laifuffuka daban-daban har 21 da ya kamata a hukunta su.

Sai dai bai bayyana laifuffukan da sojojin su ka aikata ba, amma bayanai sun nuna cewa, sojojin da aka hukunta a baya a irin wannan kotu sun aikata laifuffukan da su ka hada da fyade, da saida wa ‘yan fashi da makami makamai da barin aiki ba tare da izini ba, da sata, da cin zarafin yara da sauran su.

Ya ce ya bude kotun ne bisa ikon da ya ke da shi na karfin ofishin sa, ya na mai tabbatar da cewa ba za a nuna son kai ba.

ya kuma yi kira ga shugabanni da alkalan kotun da su yi aiki ba tare da nuna fifiko ba.

Exit mobile version