Home Labarai Rundunar Soji Ta Darkake Ƴan Bindigar Da Suka Lalata Wutar Arewa

Rundunar Soji Ta Darkake Ƴan Bindigar Da Suka Lalata Wutar Arewa

59
0
Troops Zamfara
Troops Zamfara

Wani hoton tauraron ɗan’Adam ya nuna yadda aka yi rugu-rugu da wani yanki da ke zagaye da tashar wutar lantarki da ke Shiroro inda a kwanakin baya aka samu matsalar lalacewar baban layin wutar.

A ranar Litinin ne Rundunar Sojin Saman Najeriya ta harba bamabamai ga ‘yan ta’addan da suka hana gyaran wutar lantarkin layin wutar na Shiroro zuwa Kaduna da ake zargin ‘yan bindiga da lalatawa.

Wannan harin bam da rundunar sojin ta kai na zuwa ne bayan mako guda da mataimakin shugaban majalisar dattawa ya bayyana cewa akwai wasu ‘yan bindiga da suka fara ƙoƙarin mamaye inda Babban layin wutar ya samu matsala.

Inda ya ce ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara na yin duk mai yiwuwa domin magance wannan matsala.

Leave a Reply