Fitaccen ɗan kasuwa kuma ɗaya daga cikin dattawan Arewa
Alhaji Gambo Muhammad Ɗan-Pass, ya ce rufe iyakokin
Nijeriya ya taimaka wajen kassara harkokin kasuwancin
al’ummar Arewa, musamman jihar Kano da ta ke cibiyar
kasuwanci.
Gambo Ɗan-Pass ya bayyana haka ne a Kano, inda ya ce sai da su ka ja hankalin tsohon shugaba kasa Muhammad Buhari a kan kada a rufe iyakokin Arewa, sannan bayan an rufe su ka yi kira cewa a buɗe su, amma ba a ji ba sai ga shi kasuwanci ya shiga halin ha’ula’i a Kano da yankin Arewa baki ɗaya.
Dan kasuwar ya yi nuni da cewa, hakan ta janyo hukumomin tsaro su ka shiga kame-kame, lamarin da ya ce ya kara taimakawa wajen kassara kasuwanci.
Ya ce ya kamata ‘yan kasuwar Arewacin Nijeriya su tashi tsaye a kawo gyara a kan harkokin kasuwanci da masana’antu wadanda duk sun durƙushe.
You must log in to post a comment.