Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Rufe Iyakoki: Gudaji Kazaure Ya Yi Kira Ga Gwamnati Ta Yi Tanadi

Honarabul Gudaji Kazaure, Dan Majalisar Makilai Jihar Jigawa

Honarabul Gudaji Kazaure, Dan Majalisar Makilai Jihar Jigawa

Shigo da shinkafa ‘yar waje na daga cikin dalilan da gwamnati ta ce ya zama dole a rufe iyakokin Najeriya

Batun rufe kan iyakokin Najeriya na ci gaba jawo hankalin jama’a da shan suka. Inda wasu ke ganin wannan mataki ya yi tsauri, kuma ya kamata gwamnati ta yi kyakkyawan tanadi tun kafin rufe kan iyakokin.

Amma hukumomin kasar na ganin illar barin kan iyakokin a bude ta fi ta rufewar da aka yi, kuma za a ci gaba da aiki da wannan mataki.

Honarabul Gudaji Kazaure, dan majalisar wakilai ta tarayya daga jihar Jigawa, yana cikin masu ra’ayin a yi shirin yadda ya kamata dan kaucewa shigar talaka mawuyacin hali.

Kazaure ya ce ”Muna goyon bayan tsarin gwamnati na dogaro da kan mu, amma bai kamata a dauki matakin rufe iyaka alhalin babu wani tanadi da aka yi wa talaka. Idan gwamnati na son daukar matakin sai ta wadata kasa da kayan da za a bukata a kuma saidawa talaka a farashi mai rahusa”.

Ya kara da cewa yawancin matakai irin wannan kan talakawa da suka zabe su ya ke komawa, saboda su ke shan wahala.

Gwamnati ta bakin mai magana da yawun shugaba Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu, ya ce ba a rufe iyakokin dan musgunawa ko bakantawa wani ba. Matakin zai taimakawa manoma da suke shan wahalar noma kayan abinci samun damar saida hajarsu ga ‘yan kasa.

Exit mobile version