Home Labaru Ronaldo Ya Yi Magana Kan Hamayyar Sa Da Messi

Ronaldo Ya Yi Magana Kan Hamayyar Sa Da Messi

110
0

Cristiano Ronaldo ya karyata ikirarin cewa burinsa ya sha gaban Messi a yawan samun nasarori musamman kyautar gwarzon ɗan wasan duniya.

Ronaldo na mayar da martani ne ga Editan mujallar Kwallo ta France Football Pascal Ferre wanda ya ce burin Ronaldo shi ne ya zarta Messi.

Ɗan wasan na Manchester United ya ce Ferre ya ƙirƙiri labarin ne kan wata manufar sa kan kyautar gwarzon ɗan wasan duniya da ba a bayar ba a 2020 saboda annobar korona.

A sakon da ya wallafa a shafukan sa na Facebook da Instagram kafin sanar da Messi a matsayin wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or a ranar Litinin ya ce Pascal Ferré ya yi ƙarya ne ta hanyar amfani da sunan sa domin tallar kan sa da kuma tallar jaridar da yake yi wa aiki.

A cikin saƙon, Ronaldo ya ce yana taya duk wanda ya lashe kyautar murna.

Messi, wanda ke taka leda yanzu a Paris St-Germain, a ranar Litinin ya lashe kyautar Ballon d’Or karo na bakwai, yayin da Ronaldo wanda ya karbi kyautar sau biyar ya ƙare a matsayi na shida a duniya a bana.