Romon Dimokradiyya: Za A Gabatar Da Kudurin Magance Talauci A N-Jeriya
A wani yunkuri na inganta rayuwar talaka, gwamnatin tarayya ta bayyana kudurin ta na gabatar da dokar magance talauci ga majalisar dokoki ta kasa.
Gwamnatin tarayya, ta ce ta kammala shirye-shirye aika wa majalisar dokoki kudurin da zai kawo hanyar da za a magance talauci a fadin Nijeriya.
Kwamitin da aka kafa don magance talauci, ya ce dokar za ta fara aiki nan ba da dadewa ba, ya na mai cewa yanzu haka ya na aiki a kan yadda za a gabatar da dokar ga majalisa.
‘Yan kwamitin kuwa sun hada da Sanata Lawal Yahaya,Gumau, da Muhammad Ali Wudil, da mai ba shugaban kasa shawara a kan sana’o’i Maryam Uwais.
Maryam Uwais ta ce, sun san cewa su na da kyakkyawan kwamitin da zai jajirce don ganin wannan kuduri ya tabbata, kuma tuni sun gama tsara shi kafin su hadu da majalisun biyu.