Home Labaru Romon Dimokradiyya: Dole Ne A Kauda Talauci A Fadin Nijeriya – Tinubu

Romon Dimokradiyya: Dole Ne A Kauda Talauci A Fadin Nijeriya – Tinubu

375
0

Babban jigon jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu, ya ce ci-gaba da ta’azzarar ta’addancin ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane da fashi da makami da rikicin makiyaya da manoma ya janyo hauhawar talauci a fadin Nijeriya.

Tinubu ya bayyana haka ne a Lagos, yayin gabatar da jawabi a wajen bikin ranar dimokuradiyya da ya gudana ranar Larabar da ta gabata.

Ya ce dole ne a shimfida matakan da za su kawo karshen matsanancin talauci a fadin kasar nan.

Tinubu ya ce dole ne a mike tsaye don ganin ‘yan Nijeriya sun cigaba da kwankwadar romon dimokradiya ta hanyar kauda talaucin da ya yi masu dabibayi.

A karshe ya gargadi ‘yan Nijeriya kada su manta da cewa, jin dadin dimokradiya da su ke yi a halin yanzu sadaukarwar magabata ce da su ka bada jinin su da rayuka wajen tabbatar da ci-gaban kasar nan.

Leave a Reply