Home Home RMAFC Ta Musanta Batun Karin Albashi Ga Tinubu, Shettima, Da Sauran Su...

RMAFC Ta Musanta Batun Karin Albashi Ga Tinubu, Shettima, Da Sauran Su #

119
0

Hukumar tattara kudaden shiga da lura da kasafin kudi ta Nijeriya, ta musanta rahoton da ke cewa ta amince da ƙarin albashin ‘yan siyasa da ma’aikatan ɓangaren shari’a da kashi 114 bisa 100.

A wata tattaunawa ta musamman da manema labarai, jami’in hulda da jama’a na hukumar Christian Nwachukwu, ya ce shugaba Tinubu bai kai ga amincewa da ƙarin albashin ba tukunna.

Babbar kwamishiniyar tarayya a hukumar Rakiya Tanko-Ayuba ce ta bayyana batun ƙarin albashin, lokacin da ta wakilci shugaban hukumar Mohammad Shehu wajen gabatar da rahoton ƙarin albashi ga gwamnan jihar Kebbi Nasir Idris a Birnin Kebbi.

Rakiya Tanko, ta ce an fara aiwatar da shirye-shiryen biyan kuɗaɗen da aka ƙara tun daga ranar 1 ga Janairu na shekara ta 2023, iƙirarin da kakakin hukumar ya musanta.

Nwachukwu, ya ce ba su kai ga yin maganar ba saboda har yanzu shugaban ƙasa bai sanya wa ƙudirin hannu ba, ya na mai cewa duk da cewa akwai maganar ƙarin albashin a ƙasa, hakan ba ya na nufin ya zama doka ba, tunda har yanzu shugaban ƙasa bai kai ga amincewa da ƙarin ba.

Leave a Reply