Home Labaru Ritayar Onnoghen: Masharhanta Sun Koka Da Matakin Da Shugaba Buhari Ya Dauka

Ritayar Onnoghen: Masharhanta Sun Koka Da Matakin Da Shugaba Buhari Ya Dauka

408
0

Masu sharhi a kan al’amuran siyasar Nijeriya sun nuna rashin gamsuwa da matakin da Shugaba Muhammadu Buhari ya dauka na amincewa da ritayar tsohon shugaban alkalan Nijeriya Walter Onnoghen, su na masu cewa babban nakasu ne ga yaki da cin hanci da rashawa.

A ranar Lahadin da ta gabata ne, shugaba Buhari ya amince da ritayar Walter Onnoghen, wanda aka dakatar sannan kotun da’ar ma’aikata ta same shi da laifin kin bayyana cikakkun kadarorin sa.

Lauya mai fafutukar kare hakkin dan Adam Audu Bulama Bukarti ya ce wannan mataki abin takaici ne, kuma ya  na nufin kamar an yafe masa laifin sa ne.

Babu dai wani cikakken bayani a kan dalilin da ya sa shugaban kasa ya amince da ritayar Onnoghen, sai dai tuni Majalisar Kula da Alkalai ta kasa ta yi maraba da wannan mataki.

Mataki dai ya na nufin, Walter Onnoghen zai karbi dukkan garabasar da ma’aikata ke karba idan sun yi murabus duk da laifin da aka same da shi.

Leave a Reply