Home Labaru Rikicin Zamfara: Sarakunan Gargajiya Sun Yi Barazanar Fasa Kwai

Rikicin Zamfara: Sarakunan Gargajiya Sun Yi Barazanar Fasa Kwai

470
0

A ‘yan kwanakin baya ministan tsaro, Mansur Dan Ali ya yi zargin cewa, akwai wasu manyan sarakunan gargajiya a jihar Zamfara da ke hulda da ‘yan bindiga masu kai hare-hare da satar mutane, lamarin da ya fusata sarakunan jihar har su ka kalubalanci ministan cewa ya fito fili ya bayyana wadanda ya ke zargi.

Shugaban majalisar sarakunan jihar Mai martaba sarkin Anka Alhaji Attahiru Ahmed, ya ce har yanzu su na nan a kan bakan su na kalubalantar ministan ya fito ya bayyana sarakunan da ake zargi da mu’amula da ‘yan bindigar.

Sarkin ya ce, kamata ya yi ministan ya zo ya ja kunnen sarakunan ko ya fadi abubuwan da su ka yi, ya na mai cewa idan aka kai su bango za su fasa kwai.

Sai dai zargin gwamnatin jihar Zamfara a kan sarakunan ya sha bamban da na ministan kamar yadda kwamishinan kananan hukumomi Bello Muhammed Dankande ya bayyana.

Tuni dai gwamnatin tarayya ta dakatar da ayyukan hako ma’adinai a jihar Zamfara, a daidai lokacin da rundunar sojin sama ta kaddamar da harin boma-bomai a maboyar ‘yan bindigar.